Monday 27 May 2013

MENENE AURE ?

  •                 Aure

  • Gamin Gambizar Sha’awa
    Tsakanin Ma’aurata Assalamu
    Alaikum jama’a, marhabin da
    sake haDuwar mu a cikin wannan
    fili, InshaAllah za mu tattauna kan
    matsalar gamin gambizar sha’awa
    tsakanin ma’aurata, da fatan Allah
    SWT Ya sa ya amfani ma’aurata
    da yawa, ya kuma kawo canji na
    alheri cikin rayuwar auren su,
    amin. Gamin gambizar sha’awa
    tsakanin ma’aurata wani yanayi
    ne da ke faruwa duk lokacin da a
    ka sami banbanci yanayin
    sha’awa tsakanin ma’aurata.
    Gamin gambizar sha’awa na da
    qofofi da dama ta inda ta ke
    kunno kai cikin rayuwar
    ma’aurata, misali, in sha’awar
    xaya ta fi ta xaya yawa, ko
    banbancin lokacin gabatarwa,
    yanayin gabatarwa da kuma
    banbacin abubuwan yi lokacin
    gabatarwar. Duk ta inda wannan
    matsala ta vullo, to ta kan jefa
    xaya ko duka ma’auratan cikin
    wani irin hali na qunci da qaqa ni
    ka yi. Mata ne su ka fi cutuwa da
    wannan matsalar a cikin rayuwar
    auren su sama da maza saboda
    kasancewar matsayin mace da
    irin rawar da ta ke takawa cikin
    rayuwar aure. In Maigida ya fi
    Uwargidan sa yawan buqatuwar
    sha’awa, dole ne ta yi ta haquri ta
    na yi, mafi yawan lokaci Maigidan
    ma bai san irin tsananin
    sadaukarwa da Uwargidan sa ke
    yi ba wajen ba shi haqqin shi,
    matan aure da yawa na faxar
    yadda su ke Ibadar aure don
    kawai su fita haqqin Mazan su:
    “Tunda na yi aure ban taba jin
    daxin Ibadar aure ba, yanzu
    kusan xiya na bakwai, kuma
    kullum ina cikin fargabar yin shi,
    mi ke kawo min haka?” “Ba najin
    sha’awa lokacin ibadar aure da
    miji na, ko me za mu yi ba na jin
    komai.” "Ina da matsala da
    maigida na, saboda bai yin wasa
    kafin ibadar aure, ni ko sai ina jin
    zafi, ko da yaushe ji na ke kamar
    ranar farko, haquri kawai na ke yi.
    Kuma ina son wasan, shi ne ba ya
    so. Me ye shawara, shin in rabu da
    shi ne?” Haka nan in aka rashin
    dace Uwargida ta fi Maigidan ta
    buqatuwa da sha’awa, to a nan
    ma wahalar ta fi yawa, domin
    bayan halin quncin hakan,
    wannan matsalar na kai wasu ga
    aikata ayyukan savo garin
    neman mafitar sha’awar su: “Miji
    na bai damu da yin ibadar aure
    ba ni kuwa ga shi na kasance mai
    tsananin buqatatuwa da ibadar
    auren, in abin ya dame ni sosai na
    kan kalli fina-finan turawa, shin
    yin hakan ba laifi?” -Safiya daga
    Kano. "Wata ran na kan ji
    sha’awar miji na amma sai na
    kasa gaya ma shi, kuma ina
    cutuwa, me ye mafita?" “Miji na
    ba ya son kusanta ta da Ibadar
    aure, sai mu yi wata ukku zuwa
    huxu kuma ni ina buqatar sa, ya
    zan yi dan Allah?” -Wata Baiwar
    Allah “Dan Allah Anti Nabila ki
    qara kira ga maza su runqa qoqari
    su na biya ma matan su buqatun
    su lokacin ibadar aure. Saboda ni
    dai ban yi dacen miji ba ta
    wannan fannin, ya wadatani da
    dukkan kayan qyale-qyalen jin
    daxin rayuwar duniya, amma a
    shekara bai fi ya kula ni sau ukku
    ba, na yi kuka har na gaji, na yi
    ma shi nasiha ba iyaka amma
    duk ba canji, Wallahi Anty gab na
    ke da in shiga wani hali, domin ni
    mace ce mai tsananin buqata, ki
    taimake ni da shawara dan
    Allah?” -H.Z, Kaduna Sannan su
    ma mazan su na cutuwa da shiga
    halin qaqa ni ka yi in Allah Ya yi
    matan da su ke aure ba ma su
    haquri ba ne balle har su daure su
    sadaukar da na su jin daxin don
    farantawa mazan su: "Duk lokacin
    da mu ke tare da mata ta, ba ni
    da ikon ta~a jikin ta sai ta ture
    hannu na, kuma ita har mu gama
    ibadar aure ba za ta ta~a jiki na
    ba, ba ta son ayi wasanni ko
    kadan, kuma ba ta jin nasiha.
    Wannan abin ya na damu na, a
    taimaka min da shawara." Ahmad
    Kano "Me ke sa wasu matan sai
    su runqa nuna kamar an matsa
    ma su duk lokacin da aka neme
    su, ko su faxi wata baqar
    maganar har mutum ya ji ya
    fasa? Ya za a gane irin wadannan
    mata don a kauce ma su, kuma in
    mutum ya riga ya aura menene
    mafita? Domin irin wannan ya sha
    kashe aure kuma a rasa dalilin
    mutuwar sa." Idris, Kano "Ina da
    sha’awa sosai, fahimtar haka ta sa
    aka yi min aure da wuri sai dai
    ban yi dacen mata ba, don in zan
    yi wata ban kula ta ba ko a jikin
    ta, har cika baki ta ke da hakan,
    duk sai in ji na tsane ta. In na
    neme ta, ko ta amince to ban
    gamsuwa, shekaran mu sha xaya
    amma har yau ban san daxin
    aure ba, na tava qara aure amma
    na ga duk xaya su ke, me ye
    mafita?" Daga Kano Hanyoyin
    Tafiyar da Gamin Gambizar
    Sha’awa Zan fara gabatar da
    nasiha ga mazan da matan su su
    ka fi su buqatuwa da sha’awa,
    sannan don mugunta sai su share
    su har sai ranar da su su ka
    buqace su alhali su na sane
    dahalin da su ke ciki na tsananin
    buqatuwar sha’awa, su sani
    wannan ba jarumta ba ce,
    raggwanci ne na qarshe. Ya ku irin
    waxannan Magidanta, ku sani,
    babban jigon da a ka gina aure a
    kai, shi ne saduwar ibadar aure
    don biyan buqatar sha’awar juna,
    don haka in mace ta zan ba ta iya
    gamsar da namiji ko namiji ya zan
    ba ya iya gamsar da matar sa, to
    wannan qwaqwqwaran dalili ne
    na a raba auren don ta sami wani
    wanda zai iya gamsar da ita. Cikar
    mazantakar xa namiji shi ne ya
    kasance mai gamsar da iyalan sa
    ta ko wane irin fanni na rayuwar
    su amma musamman ma ta
    fannin ibadar aure. Ku sani, rayin
    xan’adam na iya daure ma
    dukkanin buqatuwar rayuwar
    duniya, amma ban da buqatuwar
    ibadar aure saboda da tsananin
    qarfin ta da girman ta, to meye
    amfanin auren da matan na ku su
    ke yi da ku in auren bai yi ma su
    maganin tsananin buqatuwar su
    ta sha’awa ba? Sai dai su runqa
    kallon kafirai su na zina don su
    rage zafi? Dubi irin haxarin da ku
    ke tura matayen ku a ciki? In har
    ku na son su don mi ba za ku
    sadaukar da ko da sau xaya a
    wata ne ba don warkar ma su da
    tsananin buqatuwar su? Wannan
    wane irin zalunci ne a ce ka aje
    lafiyayyar mace a gidan ka
    amma sau ukku kaxai ka ke
    waiwayar ta a shekara? Duk wani
    kayan jin daxin da za ka tanadar
    ma ta na banza ne tunda ga wani
    abu da ta fi so sama da komai,
    kuma ya kasance kai kaxai ne za
    ka iya ba ta shi, amma ka hana
    ta! Kun sani akwai halattattun
    hanyoyi da dama da za ku biya
    ma matan ku buqatun sha’awar
    su ba tare da lallai sai ku kun yi
    ibadar auren ba, to in kuwa akwai
    so ai ya kamata ayi wannan
    sadukarwas, ku tuna in ku ne ku
    ke cikin hali irin wanda matan ku
    su ke ciki za ku so ayi mu ku
    haka? A ji tsoron Allah dai!
    Mazantaka ba a qira, siffa ko
    halitta ta ke ba. Mazantaka a
    qwaqwalwa ta ke, don haka in ku
    na tunanin ku cikakkun mazaje ne
    ta kowa ne fannin to haka za ku
    kasance. In kuma ku na tunanin
    kun cika mazaje ne ta fannin biya
    ma matan ku buqatun masarufi
    kaxai amma ban da buqatun su
    na sha’awa to hakan za ku
    kasance. Kuma Ibadar aure ba
    biyan buqatar sha’awa ne kadai
    ribar ta ba, ta na sanya rahama
    da tausayi tsakanin ma’aurata
    kamar yadda ayoyin Alqur’ani
    mai girma su ka yi bayani.

1 comment:

  1. আমি মোঃরকি ইসলাম । পেশায় একজন প্রবাসি। বর্তমানে মালেশিয়ায় বসবাস করছি। ব্লগ পড়তে ও আর্টিকেল লিখতে পছন্দ করি
    sad dp
    Sad status in hindi
    LOVE QUOTES IN HINDI
    what is love?
    font copy and paste
    অনলাইন কাজ

    ReplyDelete